ha_tq/mal/04/01.md

450 B

A ranar dake zuwa, ƙuna kamar tanderu, menene zai faru da masu girman kai da ma su aikata mugunta?

Masu girman kai da ma su aikata mugunta za su zama tattaka, za a ƙone su.

Ga wanene ranar adalci za ta fito wa?

Ranar adalci za ta fito wa waɗanda suke tsoron sunar Yahweh.

Menene waɗanda suke tsoron sunar Yahweh za su yi a ranar da Yahweh zai aikata?

Za su fita, su yi ta tsalle kamar 'yan maruka a dangwali kuma za su tattake mugaye.