A misalin Yesu na biyu, menene zai faru idan an dura sabon ruwan inabi a tsofaffin salkuna?
Tsofaffin salkuna zai fasa kuma sabon ruwan inabi zai zube.
Menene Yesu ya ce dole ya faru domin a ajiye sabon ruwan inabi da kyau?
Dole a sa sabon ruwan inabi a cikin sabobin salkuna.