ha_tq/jhn/12/48.md

421 B

Menene zai hukunta waɗanda sun ƙi Yesu kuma ba su ƙarbi maganarsa ba?

Kalmar da Yesu ya faɗa, ita ce za ta hukunta waɗanda sun ƙi shi a rana ta karshe.

Yesu ya yi maganar bisa kansa ne?

A'a. Uba wanda ya aiko Yesu shi ke ba shi umarni game da abin da zai ce da abin da zai faɗi.

Don menene Yesu ya ce wa mutanen kamar yadda Uban ya faɗa masa?

Yesu ya yi wannan domin ya san umarninsa rai ne madawwami.