ha_tq/jhn/03/19.md

522 B

Don menene a na sharanta mutane?

A na sharanta mutane domin haske ya zo duniya, amma mutane suka ƙaunaci duhu fiye da hasken, sabili da ayyukan su na mugunta ne.

Don menene waɗanda suke aikata mugunta ba su zuwa ga haske?

Waɗanda suke mugayen ayyuka sun ƙi haske, kuma basu zuwa wurin hasken domin kada ayyukansu su bayyanu.

Don menene masu aikata gaskiya suna zuwa ga haske?

Suna zuwa ga haske domin a iya ganin ayyukansu da kyau, kuma ya zama sananne cewa ayyukansu da ake aiwatarwa ga Allah, su bayyanu.