ha_tq/jhn/02/15.md

403 B

Menene Yesu ya yi wa masu saya da sayarwa da kuma masu canjin kuɗi?

Yayi tsumingiya da igiyoyi ya kore su duka daga cikin haikalin, duk da tumakin da shanun. Ya kuma watsar da sulallan masu canjin kuɗin ya birkitar da teburansu.

Menene Yesu ya ce wa masu sayar da tantabaru?

Yace wa masu sayar da tantabaru, "Ku fitar da waɗannan abubuwa daga nan. Ku daina maida gidan Ubana wurin kasuwanci."