Yahweh ya kira shi da suna tun daga haifuwa. Ya maida bakin Isra'ila kamar takobi mai kaifi kuma ya ɓoye Isra'ila cikin inuwar hannunsa; ya maida Isra'ila gogaggiyar kibiya; a cikin kwarinsa ya ɓoye shi.