ha_tq/isa/29/13.md

426 B

Menene gunangunin Ubangiji găba da mutanensa?

Ubangiji ya ce, ''Waɖannan mutane suna kusatowa gare ni da bakunansu, suna kuma girmamani da leɓunansu, amma zuciyarsu tana nesa da ni. Girman da suke ba ni na dokokin mutanen ne da an riga an koya.

Tun da zuciyarsu ta yi nesa da Ubangiji kuma ba su girmama shi ba, menene Ubangiji zai yi masu?

Zai sa hikimar masanansu ta lalace kuma fahimtar masu tattalinsu ta ɓace.