Da mutanen suka ga Musa ya yi jinkirin dawowa daga dutsen, sai suka taru kewaye da Haruna, suka ce masa ya yi masu gunki.