Haruna zai sa wannan tufar sa'ad da zai yi hidima, domin a iya jin ƙararta sa'anda ya ke shiga wuri mai tsarki gaban Yahweh da sa'ad da yake fita. Wannan domin kada ya mutu ne.