A dukkan ƙasar Masar kuwa, ƙankaran ta bugi kowanne abu cikin gonaki, da mutane da kuma dabbobi. Ta bugi kowacce shuka da ke a gonaki ta kuma karya kowanne itace.