ha_tq/deu/15/01.md

449 B

Menene dole Isra'ilawa su yi a ƙarshen shekaru bakwai?

A karshen shekaru bakwai Isra'ilawa dole su yafe basussuwa.

Menene ya sa kowane bashi za a yafe kowane shekara bakwai?

Kowane mai bin bashi zai yafe abin da ya ranta wa maƙwabcinsa ko ɖan'uwan sa domin an yi shelar yafe basussuwa ta Yahweh.

Daga wanene Isra'ilawa za su iya nema biyan bashi a karshen kowane shekara bakwai?

Isra'ilawa za su iya neman biyan bashi daga wurin bako.