ha_tq/dan/03/03.md

499 B

Wanene ya zo ƙaddamar da sifar da Nebukadnezzar ya yi?

Sai shugabannin sassa da yankuna da gundumomi da ma su ba da shawara da ma su ajjiya da ma su shari'a da alƙalai da dukkan manyan jami'an gundumomi, su ka tattaru domin ƙaddamar da sifar.

Menene Nebukadnezzar yake so waɗanda suka taru a wurin ƙaddamarwan su yi?

Yana so waɗanda suka taru a kadamarwan su runsuna wa sifar sa'anda su ka ji karar kaho, sarewa da garaya da molo da caki da kuge da algaita da kowanne irin kayan kiɗa.