Wanene ya hana Bulus yin wa'azi da koyarwa sa'ad da yake ɗan kurkuku a Roma na shekaru biyu?
Ba wanda ya hana shi.
Menene Bulus ya yi sa'ad da yake ɗan kurkuku a Roma?
Bulus ya yi wa'azin mulkin Allah, ya kuma yi koyarwa game da Ubangiji Yesu Almasihu da gabagadi.