ha_tq/2ti/02/08.md

452 B

Da ya rubuta wa Timoti, a wane yanayin wahala ne Bulus ya ke ciki domin wa'azin kalmar Allah da yake yi?

Bulus ya na wahala ta hanyar sarƙokin da aka ɗaura shi kamar mai laifi.

Menene Bulus yace ba a ɗaure ba da sarƙoki?

Ba a ɗaure Kalmar Allah ba da sarƙoki.

Me ya sa Bulus ya jimre wa wannan abubuwa duka?

Bulus yana jimre wa waɗannan abubuwa duka domin mutanen da Allah ya zaɓa, saboda su samu ceton da ya ke cikin Almasihu Yesu.