ha_tq/2ti/01/08.md

655 B

Menene Bulus ya gaya wa Timoti kada ya yi?

Bulus ya gaya wa Timoti kada ya ji kunyan shaida game da Ubangiji.

Menene Bulus ya gaya wa Timoti ya yi a maimakon haka?

Bulus ya gaya wa Timoti a maimakon haka ya zama mai shan wahala domin bishara.

A wane lokaci ne aka bamu shirin Allah da alherinsa?

An bamu Shirin Allah da kuma alherinsa kafin farawar lokaci.

Ta yaya ne Allah ya bayyana shirinsa game da ceto?

An bayyana shirin Allah game da ceto ta hanyar bayyanuwar mai cetonmu Almasihu Yesu.

A lokacin da Yesu ya bayyana, menene ya yi game da mutuwa da rai?

Yesu ya hallaka mutuwa, ya kuma Kawo rai da ba ya ƙarewa ta hanyar bishara.