Ziba bawan Mefiboshet ya gamu da shi da jãkai guda biyu labtattu; a kansu kuwa dunƙulen gurasa guda ɗari biyu na kurshe ɗari da 'yayan itacen ɓaure ɗari da salkar ruwan inabi ya kawo ma Dauda.