Ahaz ya ɗauki azurfa da zinariya da ke a cikin gidan Yahweh da kuma cikin taskar padar sarki, sa'anan ya aika masa a matsayin kyauta wa sarkin Asiriya.