ha_tq/2co/11/22.md

412 B

Menene fahariyar Bulus a kwatanta kansa ga waɗanda suke so a gan su daidai da shi a abin da suke fahariya?

Bulus ya yi fahariya cewa shi ba-yahuɗe ne, ɗan Isra'ila kuma zuriyar Ibrahim kamar waɗanda sun so su zama daidai da shi. Bulus ya ce shi bawan Almasihu fiye da su, ya kuma yi aiki tukuru fiye da su duka, ya shiga kurkuku fiye da kowa, a shan duka babu misali, a fuskantar haɗuran mutuwa da yawa.