ha_tq/2co/01/03.md

371 B

Ta yaya ne Bulus ya kwatanta Allah?

Bulus ya kwatanta Allah a matsayin Uba na Ubangijinmu Yesu Almasihu, Uban dukan jinƙai, da kuma Allahn dukan ta'aziya.

Don menene Allah ya na ta'azantar da mu a wahalarmu?

Yana ta'azantar da mu a cikin dukan wahalarmu, domin mu iya ta'azantar da waɗanda ke cikin kowace wahala, da irin ta'aziyar da Allah ke ta'azantar da mu.