Sun kashe ragunan Idin ketarewa , suka yayyafa jini, suka kuma cire fatar ragunan, suka kuma mika su hada yar konawa ga Yahweh, kamar yadda yake a rubuce, a cikin litafin Musa.