ha_tn/zec/14/20.md

760 B

su zama kamar kwanonin da suke gaban bagade

AT: "za su zama tsarkakakku kamar kwanonin da ake amfani da su a bagade"

Kowace tukunya da take Urushalima da Yahuza za ta zama kebabbiya ga Yahweh Mai Runduna.

Akan yi tukwane dabam-dabam da wadansu kayayyakin amfani musamman don a yi aiki da su a haikali wajen yin sujada ga Yahweh da kuma hadayu. An dauki wadannan kebabbau na musamman, ba za a more su domin wani abu dabam ba.

Ba za a kara samun masu ciniki a haikalin Yahweh Mai Runduna ba

Al'ada ce 'yan kasuwa su rika sayar wa mutane abubuwan da suke bukata domin yin hadayar da ta dace ga Yahweh a haikalin. Waɗansu juyin sun fassara zuwa "Kan'aniyawa", domin nassin Ibraniyancin yana iya zama da tagwayen ma'ana: "'yan kasuwa" da "Kan'aniyawa".