ha_tn/zec/09/14.md

1.4 KiB

Muhimmin Bayani:

Wannan bangaren anabcin ya ci gaba da kalmomin Yuhsa'u, maimakon kalmomin da Yahweh ya fada ta wurinsa.

bayyana kansa gare su

Kalmar "su" tana nufin jama'ar Allah. AT: "jama'arsa za su gan shi a sararin samaniya" ko "zai zo wurin jama'arsa"

za ta fita kamar walkiya!

Isra'ila sukan dauki walkiya a matsayin kibiyar da Allah ya harba.

busa kahon

kahonnin na raguna ne. Mutanen sukan busa su don ba da alama a lokacin yaki da kuma wadansu bukukuwa.

taho da guguwa daga Teman

Wadansu lokuta Isra'ilawa sukan yi tunanin Allah kamar yana tafiya a kan guguwa mai karfi, wacce ke zuwa daga kudu.

zai hallaka

AT: "zai yi nasara gaba daya"

nasara kan duwatsun majajjawa

Isra'ilawa za su yi nasara kan mayakan da ke yaki da majajjawa. Wadannan mayakan suna wakiltan dukkan abokan gaban Isra'ila, ko da wane irin makamai suke dauke da su.

Za su sha, su yi sowa kamar mutanen da suka bugu da ruwan inabi

AT: "Za su yi ihu suna murnar nasararsu da babbar murya, kamar sun bugu".

za su cika kamar tasar ruwan inabi

Mai yiwuwa wannan yana nufin tasoshin da firistoci suke amfani da su wajen daukan jinin dabbobi zuwa bagade. AT: "za su cika da ruwan inabi kamar tasoshin da firistoci suke daukan jini zuwa bagade"

kamar kuma kusurwowyin bagade

Bagadai suna da mikakkun kursuwoyi, inda jinin dabbobi ke taruwa. AT: "kamar yadda kusurwoyin bagade ke cika da jini"