ha_tn/zec/09/11.md

746 B

Ke kuma

A nan, "ke" yana nufin jama'ar Israila.

ramin da babu ruwa

Wannan ramin yana nuni da bauta.

Ku komo mafakar

AT: "Ku komo kasarku, inda kuke da tsaro"

daurarrun masu bege

Wannan furcin yana nuni da Isra'ilawa da suke bauta, wadanda suke sa rai Allah zai cece su.

tankwasa Yahuza kamar bakata

Ana maganar jama'ar Yahuza kamar su baka ne da Allah zai tafi yaki da ita. AT: "Zan mori jama'ar Yahuza in yaki mutanen Girka"

cika jakata ta kibau da Ifraimu

Ana maganar jama'ar Israimu, masarautar arewa, kamar su kibau ne da Allah zai harbi makiyansa. A cikin jakar kibau ake sojoji suke tara kibau.

Na ta da 'ya'yanki, Sihiyona, su yi gaba da 'ya'yanki, Girka

Allah yana magana da mutanen kasashe biyu a lokaci guda.