ha_tn/zec/09/09.md

1.1 KiB

Ki yi sowa ta farin ciki kwarai, diyar Sihiyona! Ki ta da muryarki, ɗiyar Yerusalem!

Waɗannan maganganu biyu suna nufin abu daya, kuma suna jaddada umurnin a yi murna.

ɗiyar Sihiyona ... ɗiyar Yerusalem

"Sihiyona" daya ce da "Yerusalem". Annabin yana maganar birnin kamar diya ce. Duba yadda ka fassara "ɗiyar Sihiyona" a 2:10.

bisa kan jaki, a kan aholaki

Waɗannan kalamai biyu suna nufin abu daya, kuma suna maganar dabba daya ne. Jimla na biyu ya kara bayyana cewa wannan dan aholaki ne. AT: "a kan ɗan jaki" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-doublet)

datse karusar Ifraimu

AT: "hallak karusai na Isra'ila, waɗanda ake mora domin yaki"

doki daga Yerusalem

AT: "dawakan yaki a Yerusalem"

zan kuma karya bakan yaki

A nan, baka yana wakiltan dukkan makaman yaki da ake yaki da su. AT: "za a hallaka dukkan makaman yaki"

zai furta salama ga al'ummai

A nan, aikin shelar salama yana wakiltan aikin wanzar da zaman lafiya. AT: "gama sarkinku zai kawo salama ga al'ummai"

ikonsa zai zama daga teku zuwa teku, daga Kogin zuwa matukar duniya!

"mulkinsa zai zama bisa dukkan duniya!"