1.1 KiB
Amma ba su ji ba, ba su kuwa kula ba
Duk wadannan maganganu biyu suna nufin cewa jama'ar Isra'ila sun ki su yi biyayya da umurnan Yahweh. AT: "Amma sun ki su saurari umurnaina".
wannan ce maganar Yahweh
Akan fassara wannan furcin zuwa "Yahweh ya ce" a UDB. Za ka iya fassara wannan bayanin a hanyar da fi dacewa da yarenka. An mori wannan furcin sau da yawa a Zakariya.
To, ina ubannin nan naku suke? Annabawa fa, suna nan har abada ne?
An yi wadannan tambayoyi biyun don nuna gaskiyar cewa mutane suna mutuwa. AT: "Ubanninku sun mutu. Annabawan ma za su mutu".
Amma maganata da dokokina, wadanda na umurta wa bayina annabawa, ba su tabbata a kan ubanninku ba?
An mori wannan tambayar don nuna wa jama'ar Isra'ila cewa, komai da Allah ya fada wa annabawansa su gargadi kakanninsu a kai, ya faru.
maganata da dokokina
Duka wadannan biyun suna nufin abin da Allah ya fada wa annabawan.
tabbata a kan ubanninku
Yahweh yana magana game da anabce-anabcensa kamar suna gudu ne don su shawo gaban kakannin jama'ar Isra'ila. Kalmar "tabbata a kan" tana nufin kurewa.
hanyoyinmu da ayyukanmu
"halayyaramu da al'amuranmu"