ha_tn/zec/01/01.md

1.1 KiB

A watan takwas

Wannan ne wata na takwas a kalandar Ibraniyawa. Yana a wajejen karshen Oktoba da kuma farkon watan Nuwamba a kalantar kasashen Yamma.

a shekara ta biyu ta sarautar Dariyos

"shekara ta biyu bayan Dariyos ya zama sarki"

maganar Yahweh ta zo

"Yahweh ya fadi maganarsa"

Yahweh

Wannan ne sunan Allah, wanda ya bayyana wa jama'arsa a Tsohon Alƙawari. Duba shafin fassara Kalma a kan Yahweh game da yadda za ka fassara wannan.

Berekiya ... Iddo

Wadannan sunayen maza ne (Duba: rc://*/ta/man/translate/translate-names)

tsananin fushi da ubanninku

"fushi kwarai da kakanninku"

Ku komo wurina

Ana mora kalmar "komo" don nuni da wani sauyi. Yahweh yana fada wa jama'ar Isra'ila cewa su canza daga rashin yi masa biyayya zuwa yi masa biyayya.

wannan ce maganar Yahweh Mai Runduna

Akan fassara wannan zuwa "Yahweh ya e" a UDB. Za ka iya fassara wannan bayanin a duk hanyar da ka ga ta fi dacewa a yarenka. An mori wannan furcin sau da yawa a cikin Zakariya.

zan komo wurinku

Ta wurin cewa zai komo wurin jama'ar Isra'ila, Yahweh yana cewa al'amuran alheri za su faru domin yana taimakonsu. AT: "zan albarkace ku".