ha_tn/tit/01/10.md

1.2 KiB

kangararrun mutane

Waɗannan kangararrun mutanen ne da ba su goyi bayan sakon bisharar Bulus ba.

masu fankon maganganun da masu yaudara

Wannan magana na bayyana kangararrun mutanen da aka ambata a baya. Anan "fanko" na nufin banza, kuma "masu fankon maganganu" su ne mutanen da ke maganganu banza da wofi. AT: "mutane waɗanda ke yin banzan maganganu su kuma yaudari waɗansu" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

waɗanda ke da kaciya

Wannan na nufin Yahudawan masubi waɗanda ke koyar da cewa dole ne mutane su yi kaciya don su bi Almasihu. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

Wajibi ne a hana su

"Dole ne a hana su yaɗa koyarwar su" ko "Dole ne a hana ɓata wasu ta wurin kalmomin su"

abin da bai kamata su koyar ba

Waɗannan abubuwa ne da ba daidai ne a koyar game da Almasihu ba da kuma shari'ar, domin, ba gaskiya ba ne.

saboda makunyaciyar riba

Wannan na nufin riba da mutane ke samu ta wurin aikata abubuwan da ba na halal ba.

suna rusar da iyalai ɗungum

"suna ɓata iyalai ɗungum." Ainihin zancen ita ce su na rusar da iyalan ta wurin rushe bangaskiyarsu. Mai yiwuwa wannan ya sa 'yan iyalin yin musu da juna.