ha_tn/rut/04/11.md

1.0 KiB

mutanen da suke a wurin

''mutanen da suke gamuwa a kofar ganuwar''

ta zo gidanka

Wannan na da ma'ana biyu. Wato idan Rut ta aure Boaza , za ta zo gidansa. Gida anan kuma na iya nufin zata zama daya daga iyalin Boaza idan ta aure shi. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

kamar Rahila da Lai'atu

wadanan sune matan Yakubu, da aka canza sunnan sa zuwa Isra'ila.

suka gina gidan Isra'ila

''suka haifi 'ya'ya a yawa wanda suka zama al'umman Isra'ila

ya sa ka bunkasa a cikin Efrata

Efrata shi ne sunnan kabilan da Boaza ke ciki a garin Baitalami.

ya sa gidanka ya zama kama

Allah ya albarkace Yahuda ta wurin ɗan sa Feresa. Mutanen nan suna rokon Allah ya albarkaci Boaza kamar yadda ya albarkace wadannan mutanen ta wurin 'ya'yan da Rut za ta haifa. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

Tamar ta haifa wa Yahuda

Tamar wata gwauruwa ce ita ma. Yahuda ya sami ɗa ta wurinta, wanda ya sa sunnan gidan ta cigaba.

ta wurin 'ya'yan da Yahweh zai ba ki

Yahweh zai ba ma Boaza 'ya'ya ta wurin Rut.