ha_tn/rom/15/01.md

1002 B

Mahaɗin Zance:

Bulus ya gama wannan sashin game da rayuwar masubi don wasu ta wurin tunashe su yadda Almasihu ya yi rayuwa.

Yanzu

Ku juya wannan ta wurin yin amfani da kalmomin da ake amfani da shi a harshen don gabatar sabuwar zance.

mu da muke da karfi

Anan "karfi" na nufin mutanen da ke da karfi cikin bangaskiyarsu. Sun gaskanta cewa Allah ya ba su iznin cin kowane irin abinci. AT: "mu da muke da karfin cikin bangaskiya" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)

mu

Wannan na nufin Bulus, masu karatunsa da kuma sauran masubi. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-inclusive)

raunanan

A nan "raunanan" na nufin mutanen da ke raunana cikin bangaskiyar. Sun gaskanta cewa Allah bai yarda musu su ci wasu irin abinci. AT: "waɗanda ke raunana cikin bangaskiya" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)

a gina shi

Ta wurin wannan, Bulus na nufin karfafa bangaskiyar wani. AT: "a karfafa bangaskiyarsa" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)