ha_tn/rom/14/20.md

959 B

Kada ka rushe aikin Allah saboda abinci

Ku na iya bayana ma'anar wannan jimlar a fili. AT: "Kada ka warware abin da Allah ya yi wa ɗan'uwa maibi wai domin ka na so ka ci wani irin abinci" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)

amma mugun abu ne mutumin da ya ci ya sa shi tuntuɓe

A nan abin da ke "sa shi tuntuɓe" na nufin ta na sa ɗan'uwa raunana ya yi abin da lamirinsa bai amince da shi ba. AT: "amma zai zama zunubi in wani ya ci abincin da wani ɗan'uwa ke tunanin cewa ba daidai ne a ci ba, idan ta wurin ci wannan ya sa ɗan'uwa raunana ya yi abinda lamirinsa ba amince ba" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)

Ya kyautu kada ka ci nama, ko ka sha ruwan inabi, ko wani abinda zai sa ɗan'uwanka tuntuɓe

"Zai fi kyau kada ka ci nama ko ka sha ruwan inabi ko kuwa ka yi wani abu da zai iya sa ɗan'uwanka zunubi"

ka

Wannan na nufin mai ƙarfin cikin bangaskiya, "ɗan'uwa" na nufin raunana cikin bangaskiya.