ha_tn/rom/10/11.md

1.4 KiB

Gama nassin ta ce

Bulus ya yi magana game da Nassin sai ka ce ya na a raye kuma yana da murya. Ku na iya bayyana a fili wanda ya rubuta Nassin da Bulus ya yi amfani da ita ana. AT: "Gama Ishaya ya rubuta a cikin Nassin" (Dubi: [[rc:///ta/man/translate/figs-personification]] and [[rc:///ta/man/translate/figs-explicit]])

Dukkan wanda ya gaskanta a gare shi ba za ya kunyata ba

Wannan daidai ne da : "Dukkan wanda ba gaskanta ba zai kunyata." An yi amfani da wannan don a nanaci ne. AT: "Allah zai daraja dukkan wanda ya gaskanta da shi" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)

Gama babu bambanci tsakanin Bayahude da Ba'alumme

Bulus na nufin cewa Allah zai yi da dukkan mutanen daidai. Ku na iya bayyana wannan a fili cikin juyin ku. AT: "daidai haka Allah ke yi da Yahudawa da waɗanda ba Yahudawa" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)

shi mayalwacin ne ga duk wanda ya kira gare shi

A nan "shi mayalwaci" na nufin cewa Allah zai zuɓo da yalwar albarkarsa. Ku na iya bayyana wannan a juyin ku. AT: "a yalwace ya albarkaci duk wanda ya dogara a gare shi" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)

Gama duk wanda ya kira bisa ga sunan Ubangiji zai sami ceto

Anan kalman "suna" na nufin Yesu. AT: "Ubangiji zai cece duk wanda ya dogara a gare shi" (Dubi: [[rc:///ta/man/translate/figs-metonymy]] and [[rc:///ta/man/translate/figs-activepassive]])