ha_tn/rom/09/01.md

1.0 KiB

Mahaɗin Zance:

Bulus ya bayyana muradin sa cewa al'uman Israila su sami ceto. Sa'annan ya nanata bambamcin hanyar da Allah ya shiryar musu don su gaskanta.

ina faɗin gaskiya ne cikin Almasihu. ba karya nake yi ba

Waɗannan maganganu biyun na nufin abu ɗaya ne. Bulus ya yi amfani da su don ya nanata cewa ya na faɗin gaskiya ne. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-doublet)

Lamirina, na shaida a cikin Ruhu Mai Tsarki

"Ruhu Mai Tsarki na mulkin lamirina kuma ya tabbata cewa abin nan da na faɗa"

cewa ina da matukar bakin-ciki da takaici marar karewa a zuciyata

A nan "takaici mara karewa a zuciyata" karin magana ne da Bulus ya yi amfani da ita don matsanancin baƙin cikin sa. AT: "ina gaya mu cewa ina matukar juyayi sosai da kuma zurfin" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-idiom)

matukar bakin-ciki da takaici marar karewa

Waɗannan maganganu biyun na nufin abu ɗaya ne. Bulus ya yi amfani da su tare don ya nanata matukar shauƙinsa take. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-doublet)