ha_tn/rom/06/01.md

1.4 KiB

Mahaɗin Zance:

A karkashin alheri, Bulus ya faɗa wa waɗanda suka gaskanta da Yesu cewa su yi sabon rayuwa kamar su mattattu ne ga zunubi da kuma rayayyu ne ga Allah.

Me kuwa zamu ce? Sai mu ci gaba da yin zunubi domin Alheri ya yawaita?

Bulus ya yi waɗannan tambayoyi nan don ya jawo hankalin masu karatunsa ne. AT: "To, me za mu ce game da duk wannan? Haƙika ba za mu cigaba da yin zunubi ba wai don Allherin Allah ya yawaita ba! (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)

mu ce

kalman nan "mu" na nufin Bulus, masu karatun sa da sauran mutane. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-inclusive)

mu da muka mutu cikin zunubi mu ci gaba da rayuwa cikin sa?

A nan "mutu cikn zunubi" na nufin cewa masubi Yesu su na kamar mattattun mutane ne wanda zunubi ba za ta iya shafe su ba. Bulus ya yi amfani da wannan tambayar don nanaci ne. AT: "Muna kamar mutanen da zunubi ba ta shafe su ba! Don haka ba za mu cigaba da zunubi ba!" (Dubi: [[rc:///ta/man/translate/figs-metaphor]] and [[rc:///ta/man/translate/figs-rquestion]])

Ba ku san cewa duk waɗanda aka yi masu baftisma cikin Almasihu Yesu an yi masu baftisma har ya zuwa mutuwarsa ne ba?

Bulus ya yi amfani da wannan tambaya don ya kara nanaci. AT: "Tuna fa, a sa'adda an yi mana baftisma don a nuna cewa muna da ɗangantaka da Almasihu, wannan kuma na nuna cewa mun mutu tare da Almasihu a kan giciye!" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)