ha_tn/rom/05/12.md

888 B

ta wurin mutum ɗaya zunubi ya shigo ... mutuwa ta shigo ta dalilin zunubi

Bulus ya bayyana zunubi kamar wani abu ne mai hatsari da ta shigo cikin duniya ta wurin aikin "mutum ɗayan nan" wato Adamu. Wannan zunubi kuwa ta zama kofa wadda mutuwa, wadda ke nuna hoton wani abu kuma mai hatsari, ta shigo duniya. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-personification)

Domin kuwa tun kafin a bada shari'a, zunubi na nan a duniya

Wannan na nufin cewa mutane su na zunubi tun kafin Allah ya bada shari'ar. AT: "Mutanen suna zunubi tun kafin Allah ya ba wa Musa shari'ar" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)

amma ba' a lissafin zunubi in da ba shari'a

Wannan na nufin cewa Allah bai lisafta wa mutane zunubansu ba kafin a ba da shari'ar. AT: Amma Allah bai rubuta zunubi gaba da shari'ar ba kafin ya bada shari'ar" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)