ha_tn/rom/02/21.md

1.2 KiB

To kai mai koyawa waɗansu, ba ka koyawa kanka?

Bulus yana amfani da tambaya domin ya kwaɓe masu sauraronsa. AT: "Kana koyawa waɗansu, amma ba ka koyar da kanka!" ko "kana koyawa waɗansu amma ba ka aikata abin da kake koyarwa!" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)

Kai da kake wa'azin kada a yi sata, shin, kai ba ka yi ne?

Bulus yana amfani da tambaya domin ya kwaɓe masu sauraronsa. AT: "Kana cewa mutane kada su yi sata, amma kai kana sata!" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)

Kai mai cewa kada a yi zina, shin kai ba ka yi ne?

Bulus yana amfani da tambaya domin ya kwaɓe masu sauraronsa. AT: "Kana cewa mutane kada su yi zina, amma kai kana zina!" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)

kai mai ƙyamar gumaka, shin ba ka sata a ɗakin gunki ne?

Bulus yana amfani da tambaya domin ya kwaɓe masu sauraronsa. AT: "Kana cewa wai kana ƙyamar gumaka, amma kana sata a ɗakin gunki!" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)

sata a ɗakin gunki

Ma'ana mai iya yiwuwa suna kamar haka 1) "satan abubuwa daga ɗakin gunkin al'umma su kuma sayar don su sami riba" ko 2) "kada ku aika kuɗi dake na Allah zuwa haikalin da ke a Urushalima."