1004 B
waɗanda aka gayyace su
AT: "mutanen da Allah ya gayyata" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)
bikin auren Ragon
A nan mala'ikan ya yi maganar haɗuwar Yesu tare da mutanensa har abada kamar bikin aure ne. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)
Na faɗi a gaban kafafunsa
Wannan ya na nufin cewa Yahaya ya kwanta a ƙasa ya kuma miƙa kansa don girmama ko biyaya. Waɗannan muhimman ayyuka ne a sashin sujada, don nuna biyaya ko bauta. Dubi rubutu a cikin 19:3.
'yan'uwanka
Kalmar "'yan'uwa" anan na nufin dukkan masubi, maza da mata.
waɗanda ke riƙe da shaida game da Yesu
A nan "riƙe" na matsayin gaskatawa ko sanarwa. AT: "waɗanda ke faɗan gaskiya game da Yesu" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)
domin shaida game da Yesu shine ruhun annabci
A nan "ruhun annabci" ya na nufin Ruhu mai Tsarki na Allah. AT: "don Ruhun Allah ne na ba mutane ikon faɗan gaskiya game da Yesu" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)