ha_tn/rev/12/10.md

1.2 KiB

Ni

Kalmar "Ni" na nufin Yahaya.

na ji wata murya mai ƙara a sama

Kalmar "murya" ya na nufin wanin da ya ke magana. AT: "Na ji wani ya na magana da ƙarfi daga sama" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

Yanzu ceto ya zo, ƙarfi, da mulkin Allahnmu, da iko na Almasihunsa

An yi maganar ceton mutane da Allah ya na yi ta wurin ikonsa kamar cetonsa da ikonsa abubuwa ne da sun zo. An yi maganar mulkin Allah da ikonsa kamar sun zo ne. AT: "Yanzu Allah ya ceci mutanensa da ikonsa, Allah ya na mulki kamar sarki, kuma Almasihunsa ya na da dukka iko" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

ya zo

"ya soma kasancewa" ko "ya bayyana" ko "ya zama gaskiya." Allah ya na bayyana waɗannan abubuwa domin lokacin da zai faru ya "zo." Ba wai ba su kasance tun farko ba ne.

an jefar da mai sarar 'yan'uwanmu a ƙasa

Wannan ne diragon da an jefa a cikin 12:0.

'yan'uwanmu

An yi maganar 'yan'uwa masubi kamar su 'yan'uwa ne. AT: "'yan'uwanmu masubi" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

dare da rana

An yi amfani da waɗannan sashen ranaku domin a nuna "dukka lokaci" ko "da rashin dainawa" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-merism)