ha_tn/rev/10/01.md

942 B

Muhinmin Bayani:

Yahaya ya fara bayanin wahayin babban mala'ika da yake riƙe da littafin. A wahayin Yahaya, yana kallon abin da ke faruwa a duniya. Haka ya faru ne a tsakanin busa ƙaho na shida da na bakwan.

Yana lullube cikin girgije

Yahaya ya yi magana game da mala'ikan kaman ya saka gajimare ne a matsayin kayan sa. Ana iya gane wannan bayanin ta wurin magana ne. Ko da shike, domin ba kullum bane ake ganin abubuwan a cikin wahayi, za a iya gane wannan cikin yanayin rubutu. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

Fuskar shi kamar rana

Yahaya ya kwatanta hasken fuskarsa da hasken rana. AT: "Fuskarsa da haske kamar rana" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-simile)

kafafunsa kamar ginshiƙan wuta

AT: "Kafafunsa suna kamar ginshiƙan wuta"

sai ya sa ƙafarsa ta dama a bisa teku, ƙafarsa ta hagu kuma a kan ƙasa

"Ya tsaya da ƙafar shi na dama a bisa teku, ƙafar shi na hagu kuma a kan kasa"