ha_tn/rev/09/03.md

1.4 KiB

fara

taron ƙwari da suke yawo tare a sama. Mutane na tsoron su domin su kan ci duk ganyaye na lambu ko na kan itace. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/translate-unknown)

iko kamar na kunamai

kunamai suna da gwanin harbi, kuma dafi ne ga sauran dabbobi da kuma mutane. AT: "gwanin harbin mutane kamar kunamai" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)

kunamai

ƙananan ƙwari masu dafi suna harbi ne da wutsiyar su. Harbin su na da zafi sosai har ma ya kan kai tsawon lokaci. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/translate-unknown)

Aka gaya masu kada su yi wa ciyayi da kowanne koren ganye ko itace illa

Fara da ake gani kullum mugun hatsari ne ga mutane domin idan suka taru, su kan ci duk ciyayi ko ganyaye da aka shuka da kuma na itace. An gaya ma faran kada su yi haka.

sai dai mutanen

An iya gane kalmomin nan "yin ɓarna" ko "yin illa". AT: "sai dai su yi wa mutanen illa" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-ellipsis)

hatimin Allah

Kalmar nan "hatimi" a nan na nufin kayan aiki da ake amfani domin saka alama ta wurin buga shi a kan wani abu mai kama da kakin zuma. A wannan yanayi, za a mori wannan kayan aiki domin saka alama a kan mutanen Allah. AT: "hatimi" [Wahayn Yahaya 7:3] "abin saka alamar Allah" ko "abin buga hatimin Allah" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

goshin

Goshin na bisa fuskan ne, a saman idanu.