ha_tn/rev/06/12.md

1.0 KiB

hatimi na shida

"hatimi na gaba" ko "hatimi lamba ta shida" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/translate-ordinal)

kamar baƙar tufa

Wasu lokatai, ana yin tufa da bakar gashi ne. Mutane na saka tufa yayin da suke makoki. An yi amfani da wannan ne domin ya saka mutane tunani akan mutuwa da kuma makoki. AT: "baƙa kamar kayan makoki" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-simile)

kamar jini

An yi amfani da "jini" domin ya jawo hankalin mutane su yi tunani a kan mutuwa. Za a iya bayyana wa mutane a fili, yadda take nan kamar jini. AT: "jawur kamar jini" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-simile)

kamar yadda itacen ɓaure ke karkaɗe 'ya'yansa da basu nuna ba, yayin da babbar iska ke kaɗawa

AT: "kamar yadda babbar iska take kaɗa itacen ɓaure ta saukar da ɗanyun 'ya'ya" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)

Sama kuma ta ɓace kamar littafi da aka nannaɗe

An cika yin tunanin sama kamar tana da ƙarfi kamar ƙarfe, amma yanzu kamar takarda mara ƙarfi ce aka yi maganarn ta wanda nan da nan akan yaga a kuma naɗe.