ha_tn/rev/05/09.md

693 B

Domin an yanka ka

AT: "Domin sun yanka ka" ko "Domin mutane sun kashe ka" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)

yanka

Idan yaren ka ya na da wata kalma na kashe dabba domin yin haɗaya, za ka iya yin amfani da shi a nan.

da jininka

Da shike jini na nufin rai na mutum ne, rashin jini kuma na nufin mutuwa ne. Mai yiwuwa wannan na nufin "ta wurin mutuwar ka" ko "tawurin mutuwa." (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

ka saya wa Allah mutane

"ka sayi mutane domin su zama na Allah" ko "ka biya farashin domin mutane su zama na Allah"

daga kowacce kabila, harshe, jama'a da al'umma

Wannan na nufin ya shafi kowane mutane na kabilu dabam-dabam.