ha_tn/rev/05/03.md

837 B

a sama ko a ƙasa ko ƙarƙashin ƙasa

Wannan na nufin kowane wuri: wurin rayuwar Allah da mala'ikunsa, wurin rayuwar mutane da kuma dabbobi, da kuma inda mattatu suke. AT: "ko'ina a sama ko kasa ko ƙarƙashin ƙasa" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-merism)

Duba

"Ka ji" ko "Kasa kunne ga abin da nake shiri in faɗa maka"

Zaki na kabilar Yahuza

Wannan laƙabi ne da Allah yayi wa mutum daga kabilar Yahuza, zai zama babban sarki. AT: "Wanda ake kira Zaki na kabilar Yahuza" ko "Sarki da ake kira Zaki na kabilar Yahuza"

Zaki

Ana magana game da wannan sarki kamar shi zaki ne domin zaki na da ƙarfi kwarai. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

Tushen Dauda

Wannan laƙabi ne na wanda da Allah ya yi wa zuriyar Dauda alkawali cewa zai zama babban sarki. AT: "wanda ake ce da shi Tushen Dauda"