ha_tn/rev/04/09.md

1.4 KiB

shi da ke zaune bisa kursiyin, wanda ke raye har abada abaɗin

Wannan mutum ɗaya ne. Wanda ke zaune a kursiyin na rayuwa har abada abadin.

har abada abadin

Kalmomi biyun nan na ma'anar abu guda ne kuma ana sake faɗan sune domin a nanata magana. AT: "na har abada" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-doublet)

faɗi da fuskokinsu a ƙasa

Da dalili suka kwanta da kawunansu ƙasa domin su nuna cewa suna sujada ne.

Suka jefar da kambinsu a gaban kursiyin

Wannan na kama ne da furen da ke fita a itacen zaitun ko ganyen laurel, wanda aka yi shi da zinariya. Dattatan nan sun ajiye rawanin su a ƙasa da biyayya; wannan ya nuna cewa suna miƙa kai ga ikon Allah ya yi mulkin su." AT: "suka ajiye rawanin su a gaban Allah domin su nuna cewa suna miƙa kai ga shi" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/translate-symaction)

jefar

AT: 1) a ajiye abu, ko 2) a yer da abu na dole, kamar mara amfani ne. ("wurgar," [Wahayin Yahaya 2:22])

Ubangijinmu da Allahnmu

"Ubangijinmu da Allahnmu." Wannan mutum guda ne, wanda ke zaune a bisa kursiyin.

karɓi yabo da ɗaukaka da iko

Waɗannan abubuwan ne Allah yake da su kullum. An yi maganan yabon shi domin yana da su kamar karɓan su ne yake yi. AT: "ka karɓi yabo domin ɗaukakar ka, girma, da kuma iko" ko "saboda kowa ya baka yabo domin kai mai ɗaukaka ne, mai girma ne, kuma mai iko ne" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)