ha_tn/rev/02/26.md

1.2 KiB

Zai yi mulkin ... farfasa su kamar randunan yumbu

Wannan annabci ne daga Tsohon Alkawali game da Sarkin Isra'ila, amma Yesu ya yi amfani da shi a nan domin waɗanda ya ba su iko a kan al'umai.

Zai yi mulkin su da sandar ƙarfe

Ana magana game da matsanacin mulki kamar mulki ne da sandar karfe. AT: "Zai yi mulkin su da tsanani kamar yana buga su ne da sandar ƙarfe" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

zai farfasa su kamar randunan yumbu

Farfasa su zuwa 'yan gutsure hoton ne da yake nufin 1) hallakar da masu aikata miyagun abubuwa ko 2) yin nasara da abokan gaba. AT: "Zai yi nasara a kan abokan gabansa kamar yana farfasa randunan yumbu ne" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-simile)

Kamar yadda na karɓa daga wurin Ubana

AT: 1) "Kamar yadda na karɓi iko daga wurin Ubana" ko 2) "Kamar yadda na karɓi tauraron asubahi daga wurin Ubana" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)

Ubana

Wannan suna mai muhinminci ne na Allah da yake bayyana dangantaka tsakanin Allah da kuma Yesu. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/guidelines-sonofgodprinciples)

Ni kuma zan bashi

"shi" a nan na nufin wanda yayi nasara.

tauraron asubahi

Wannan tauraro ne mai haske da ke bayyana da asuba kafin gari ya waye. Alama ce tanasara.