ha_tn/rev/02/08.md

1.1 KiB

Samirna

AT: Wannan suna ne na birni a yammacin Asiya da a yau ake ƙira Turkiya [1:11](Dubi: rc://*/ta/man/translate/translate-names)

farkon da kuma karshen

AT: Wannan na nufin kasancewar Yesu na har abada [1:17](Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-merism)

Na san wahalun ka da talaucin ka

"Wahallu" da kuma "talauci" ana iya fasara su kaman aiki ne. AT: "Na san yadda ka sha wahala ka kuma talauce" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-abstractnouns)

Nasan masu ɓata suna waɗanda suke cewa su Yahudawa ne

"Ɓata suna;" ana iya fasarar wannan kamar aiki. AT: "Na san yadda mutane sun ɓata maka suna-waɗanda suka ce su Yahudawa ne" ko "Na san yadda mutane sun faɗi munanan abubuwa game da kai-waɗanda suka ce su Yahudawa ne" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-abstractnouns)

amma ba haka suke ba

"amma su ba asalin Yahudawa bane"

majami'ar Shaiɗan

Ana magana game da mutanen da suka taru domin su yi biyaya ko ɗaukaka Shaiɗan kamar su majami'a ne, wurin sujada da kuma koyaswan domin Yahudawa. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)