ha_tn/psa/120/003.md

1.1 KiB

Ta yaya zai hore ka, mene ne kuma zai ƙara yi maka, kai wanda ke da harshe na ƙarya?

Marubuci ya roki wannan kamar tambaya mai jagora ne don bayyana abin da Allah zai yi da makaryata. Wannan tambaya za'a iya fassara ta kamar yadda a bayyani. AT: "Wannan shine yadda Allah zai horar da kai, kai wanda ka ke da harshen karya" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)

kai wanda ke da harshe na ƙarya

A nan "harshe na ƙarya" na gabatad da mutum wanda yana maganar karya. AT: "Kai wanda ke faɗin karya" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-synecdoche)

Zai hore ka da kibiyoyin mayaƙi

Marubuci ya yi magana game da Allah na horo mai tsanani makaryata sai ka ce Allah yana harbin su da kibiyoyi. AT: "Zai hore ka mai tsanani, sai ka ce yana harbin ka da kibiyoyin mayaƙi" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

wãsa bisa garwashin wutar ƙiraren itace

Wannan na nufin da yadda mutane kan kirkira bakin marshi a cikin wuta. Wannan za'a iya bayyana ta cikin fom mai kuzari. AT: "cewa ya wãsa bisa garwashin wutar ƙiraren itace" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)