ha_tn/psa/089/024.md

973 B
Raw Permalink Blame History

ta wurin sunana zai yi nasara

Anan "suna" yana wakiltar ikon Allah. AT: "Ni, Allah, zan sa shi ya zama mai nasara" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

Zan ɗora hannunsa a kan teku, hannunsa na dama kuma bisa koguna

Anan "hannu" da "hannun dama" suna wakiltar ƙarfi da iko. A nan “teku” kamar tana nufin Tekun Bahar Rum da ke yamma da Israila, kuma “koguna” suna nufin Kogin Yufiretis a gabas. Wannan yana nufin Dauda zai mallaki komai tun daga teku har zuwa kogin. AT: "Zan ba shi iko a kan komai tun daga Tekun Bahar zuwa Kogin Yufiretis" (Duba: [[rc:///ta/man/translate/figs-metonymy]] da [[rc:///ta/man/translate/figs-merism]])

Zai yi kira gare ni yace kai ne ubana, 'Kai ne Ubana kuma Allahna, da kuma dutsen cetona

Wannan yana da zance a cikin ambato. Ana iya bayyana shi azaman zance na kai tsaye. AT: "Zai ce ni Ubansa ne, Allahnsa, da dutsen cetonsa." (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-quotesinquotes da rquestion)