ha_tn/psa/034/012.md

721 B

Wanne mutum ne mai biɗar rai ya ke kuma ƙaunar ranaku masu yawa, domin ya ga alheri?

Amsar a bayyane ga wannan tambayar ita ce "kowane mutum." Ana iya fassara wannan tambayar ta lafazi a matsayin sanarwa. AT: "Kowane mutum yana son rayuwa kuma yana son rayuwa tsawon kwanaki kuma ya sami rayuwa mai kyau" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)

To, sai ka tsare harshenka daga faɗin mugunta

A nan "harshe" yana nufin mutum dukka. AT: "Saboda haka, kada ku faɗi mugunta" (Duba rc://*/ta/man/translate/figs-synecdoche)

leɓunanka kuma daga faɗin ƙarya

A nan “leɓɓa” na nufin mutumin da yake magana. AT: "kar kuyi magana da karya" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-synecdoche)