ha_tn/psa/023/001.md

1.1 KiB

Yahweh makiyayina ne

Marubucin yayi magana game da Yahweh kamar makiyayi. Wannan ya nanata yadda Allah yake kulawa da mutane kamar yadda makiyayi yake kulawa da tumakinsa. AT: "Yahweh kamar makiyayi ne a gareni" ko "Yahweh yana kula da ni kamar yadda makiyayi ke kula da tumakinsa" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

ba zan rasa komai ba

Ana iya bayyana wannan a cikin tsari mai kyau. AT: "Ina da duk abin da nake buƙata" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-litotes)

Yana sa ni in kwanta a cikin korayen makiyayu

Marubucin yana magana ne game da kansa kamar tunkiya, kuma yana magana game da Yahweh kamar makiyayi. AT: "Yana ba ni hutawa kamar makiyayi wanda ke jagorantar tumakinsa don hutawa a cikin makiyaya masu ciyayi" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

yana bi da ni kurkusa da kwantaccen ruwa

Marubucin yana magana ne game da kansa kamar tunkiya, kuma yana magana game da Yahweh kamar makiyayi. AT: "yana tanadar min da abin da nake buƙata kamar makiyayi wanda ke jagorantar tumakinsa a gefen ruwa mai nutsuwa" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)