ha_tn/psa/014/007.md

611 B

Oh, dama ceton Isra'ila zai zo daga Sihiyona!

Wannan kirari ne. Marubucin yana fadar abin da yake so ko kuma fatan Allah ya yi. AT: "Ina fatan dai ceton Isra'ila ya zo daga Sihiyona!" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

Yakubu zai yi murna, Isra'ila ma zata yi farinciki

Waɗannan jimlolin guda biyu suna nufin abu ɗaya. Anan dukka "Yakubu" da "Isra'ila" suna wakiltar mutanen Isra'ila. Za a iya haɗa jimloli biyu a cikin fassarar. AT: "to duk jama'ar Isra'ila za su yi murna ƙwarai" (Duba: [[rc:///ta/man/translate/figs-parallelism]] da [[rc:///ta/man/translate/figs-synecdoche]])